'Yan IS sun kai hari garin Marea a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Syria na cewa ana gwambza mummunan fada a arewacin kasar yayin da mayakan IS suka yi kokarin kwace garin Marea da ke hannun yan tawaye.

Mayakan IS sun kaddamar da farmaki da sanyin safiya inda suka kai harin da tankokin yaki da kuma motoci da suka sanyawa bama bamai.

Wannan ya biyo bayan kutsen da kungiyar ta rika yi a yankin tun a ranar Juma'a.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin ya ritsa da fararen hula wadanda ke kokarin tserewa.

Haka kuma akwai damuwa game da makomar mutane fiye da dubu 160 da suka tagaiyara wadanda suka nemi mafaka a kusa da kan iyakar Turkiyya.