Nigeria: Uwa ta yanka ɗanta a Damaturu

Image caption Ana samun yawan kisa a jihar Yobe.

Wata mace ta yanke kan jaririnta da wuka ta kuma binne a ramin da ta tona a cikin gidanta, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Wani dan jarida a birnin ya shaidawa BBC cewa rundunar 'yan sandan jihar sun tabbatar da afkuwar hakan.

Wani mazaunin birnin, Baana Damaturu wanda kuma yana daga cikin wadanda suka karbe wukar da ke hannun matar, ya shaidawa BBC yadda al'amarin ya faru.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti