BH: Bam ya kashe mutum 4 a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Har yanzu dai akwai burbushin 'yan Boko Haram

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu sannan wasu uku suka jikkata sakamakon tashin wani bam, da safiyar Lahadi a Biu da ke jihar Borno.

A wata sanarwa, mai magana da yawun hedikwatar tsaron Najeriya, Sani Usman Kuka-sheka, ya ce bam din ya tashi ne sakamakon hawa kansa da wani Keke Napep ya yi bisa rashin sani.

Mutane hudun da suka mutu sun hada da wata mata da 'yarta da kuma wasu maza guda biyu, a inda kuma aka samu soja guda daya a cikin mutane ukun da suka jikkata.

Sanarwar ta ce an dana bam din ne a bakin titin Biu zuwa Damboa, kusa da shingen da sojoji suka sa, a wajen garin na Biu.

Tundai bayan da mutane suka fara komawa garuruwansu sakamakon kwato da sojoji suka yi, ake samun irin wadannan tashe-tashen bama-bamai da nakiyoyi wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne suka daddasa.

Sai dai kuma Jibril Ibrahim Biu wanda mazaunin garin na Biu ne kuma ya ce abin ya faru a kan idanunsa, ya ce mutane shida ne suka rasu.

Ya kuma kara da cewa wasu mutane ne da ake zargin 'yan kunar bakin wake suka tayar da bam din a shingen da sojoji suke sanyawa. Ga dai abin da ya shaidawa BBC.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti