Ana alhini kan yaƙin Verdun

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana sa ran Hollande da Merkel za su yi kira da a samu haɗin kai a kasashen Turai.

Shugaban Faransa Francois Hollande da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na yin alhinin cika shekara 100 na yaƙi mafi tsawo da aka yi a lokacin yakin duniya na ɗaya.

Dubun-dubatar sojojin Faransa da na Jamus sun rasa rayukunsu a watanni 10 da aka shafe ana yaƙi a arewa maso-gabashin Faransa.

Daga ƙarshe sai kasar Faransa ta yi nasara a yaƙin.

Amma a yanzu ana ganin Verdun a matsayin wata alama ta sulhu tsakanin 'yan ƙasar Faransa da Jamus kuma ana sa ran Mista Hollande da Ms Merkel za su yi kira da a samu haɗin kai a kasashen Turai.