'Yan Iran ba za su je Hajjin bana ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iran ta dorawa Saudiyya alhakin turmutsutsun da aka yi lokacin aikin Hajjin bara.

Ministan al'adun kasar Iran ya ce ba za su tura 'yan kasarsu aikin Hajji a wannan shekarar ba.

Ali Jannat ya ce ba zai yiwuwu 'yan Iran su yi aikin Hajjin ba, yana mai zargin Saudiyya da yin kafar-ungulu ga 'yan Iran da ke so su yi aikin Hajjin.

A lokacin Hajjin bara ne dai daruruwan mahajjata suka rasa rayukansu kuma akasarinsu 'yan Iran ne a turmutsitsin da aka samu wanda kasar Iran din ta dora alhakin hakan kan hukumomin Saudiya.

Ana ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen guda biyu, a yayin da kasashen ke marawa yankunan da ke yaki daban-daban baya, cikinsu har da Syria da Yemen.