Lufthansa zai daina zuwa Venezuela

Hakkin mallakar hoto AFP

Kamfanin jirgin saman Lufthansa na kasar Jamsu ya ce zai dakatar da zirga-zirga zuwa Venezuela, wadda ke ƙara fuskantar koma bayan tattalin arziki.

Kamfanin ya ce matakan taƙaita hada-hada da kudaden kasashen waje sun sa ba za su iya canza kuɗin shigarsu zuwa Dala ba.

Ya ƙara da cewa buƙatar masu zuwa Venezuela ta ragu a shekarar 2015 da watanni huɗun farkon wannan shekarar.

Venezuela, wadda ƙasa ce da ke da ɗimbin arziƙin mai, tana fuskantar matsalar hauhawar farashi da ƙarancin kayan masarufi.