'Yan gudun hijira 700 sun nutse a Bahar Rum'

Hakkin mallakar hoto Marina Militare via AP Photo
Image caption Sojijin ruwan Italiya sun dauki hoton kwale-kwalen a lokacin da yake kifewa.

Majalisar dinkin duniya ta ce ta yi amanna 'yan gudun hijira 700 ne suka nitse a tekun Bahar Rum cikin kwana uku da suka wuce.

Kakakin hukumar da ke bayar da agaji ga 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, Carlotta Sami, ta ce kwale-kwalen da ke dauke da 'yan gudun hijirar sun nitse a gabashin Italiya a ranakun Laraba da Alhamis da kuma Juma'a na makon jiya a lokacin da 'yan gudun hijirar ke kokarin tsallakawa Turai.

Sojojin ruwan Italiya sun dauki hoton daya daga cikin kwale-kwalen da suka kife, kuma sun ceto da dama daga cikinsu.

An yi amannar cewa har yanzu kimanin mutum 100 da ke cikin kwale-kwalen sun bata.