Za a yi wa Boko Haram taron-dangi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin hadin-gwiwa sun sha alwashin murkushe 'yan Boko Haram.

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun ce an hada gangami domin kai farmaki kan mayakan kungiyar Boko Haram.

Ministan tsaron kasar, Hassoumi Massaoudou, ya shaida wa BBC cewa an hada sojojin kasashe makwabta, kuma a shirya suke su kara da mayakan kungiyar.

Ya kara da cewa Niger da sauran kawayenta sun yi shirin kai wa Najeriya dauki har cikin kasar.

Niger da Nigeria da Kamaru da Chadi dai sun dade suna hada-gwiwa ta fuskar dabarun yaki da kungiyar Boko-haram, wadda mayakanta ke kai hare-hare a kan al'umomin da ke iyakokin kasashen.

A hirar su da BBC, Ministan tsaron kasar Hassoumi Massaoudou ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa rundunar hadin gwiwar kasashen yankin zai wuya ta kawo karshen barazanar tsaron da yankin ke fuskanta, inda ya ce dakarun yankin sun samu horon da ya dace wajen tunkarar dukkan kalubale domin tabbatar da tsaro a yankin.