Kada ya cinye wata mata a Australia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rahotanni sun ce matar tana yin ninkaya ne tare da kawayenta lokacin da lamarin ya faru.

Ana fargabar cewa wata mata ta mutu bayan wani kada ya kai mata farmaki a gidan ajiye namun dajin Daintree na kasar Australia.

Rahotanni sun ce matar, mai shekara 46, tana yin ninkaya ne tare da kawayenta ranar Lahadi da yamma a jihar Queensland lokacin da lamarin ya faru.

Kafafen watsa labarai sun ce matar tana cikin ruwa iya ƙugu lokacin da kadan ya kai mata farmaki.

Kakakin rundunar 'yan sanda Russell Parker ya ce suna cike da fagaba game da rayuwar matar.

Ya kara da cewa, "Kawarta mai shekara 47 ta yi kokarin kubutar da ita amma hakan ya gagara. Daga nan ne ta ta ruga a guje zuwa wata kasuwa da ke kusa inda ta rika neman dauki."