EDPS: Yarjejeniyar tsare sirrin EU-US na da rauni

Tutar Tarayyar Turai

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Tutar Tarayyar Turai

Jami'in da ke da alhakin tsare sirrin bayanan al'umar Turai a intanet, Giovanni Buttarelli ya ce yarjejeniyar da Tarayyar Turai ta cimma da Amurka ta tsare sirrin al'umar Turai da ke Amurka tana bukatar gyara.

An dai cimma yarjejeniyar ne domin ta maye gurbin wadda aka kulla da kamfanin Safe Harbour, wadda kotun Tarayyar Turai ta soke a shekarar 2015.

Mr Buttarelli ya ce "na yaba da kokarin da ake yi wajen samun mai maye gurbin Safe Harbour, amma irin kariya da aka tsara ba ta da armashi."

Jami'in, a cikin wata sanarwa ya ce ba nufinsa ba ne a soke yarjejeniyar, amma yana goyon bayan matsayin da hukumomin Tarayyar Turai da ke da hakkin tsare sirri suka bayyana a watan Afrilu.

Kungiyar Tarayyar Turai ta haramta aika bayanan jama'a daga Turai zuwa wata kasar da ba ta yi kyakkyawan tanadi na tsare sirrin jama'a ba.

Bankadar da jami'in kamfanin kwarmaton wikileaks, wato Edward Snowden ya yi ya sanyaya gwiwar kungiyar Tarayyar Turai dangane da amannar da ta yi da kamfanin Safe Harbour.