Kungiyoyin kwadago na bore a Faransa

Hakkin mallakar hoto

Al'umomin Faransa za su kwashe mako guda suna fama da rikici, kasancewar kungiyoyin kwadagon sun ci gaba da boren da suke yi na kin amincewa da wasu sauye-sauye da mahukunta ke shirin yi.

A ranar Talata ne matuka jiragen kasa suka fara yajin aiki, wanda ake ganin cewa zai kara dagula harkar sufuri, kasancewar ana fama da karancin mai.

A ranar Alhamis mai zuwa ne ma'aikatan jiragen kasa da ke cikin birnin Paris za su fara nasu yajin aikin, wanda idan aka fara sai abin da Allah ya yi, yayin da matuka jiragen saman Air France su ma ke shirin shiga yajin aikin neman karin albashi a daidai lokacin da Faransar ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Turai.

Kungiyoyin kwadago sun fara maganar karin kudi, wato Euro, kuma wannan ba karamin matsin-lamba ba ne ga gwamnati musamman yadda za ta samu mafita.

'Babu gudu ba ja da baya'

Tuni dai Firayim Ministan kasar Manuel Valls ya fasa wani bulaguron da ya yi niyyar kai wa Canada.

Shugaban kasar ta Faransa Francois Hollande ya jaddada aniyarsa cewa ba zai ja da baya ba game da shirinsa na yi wa dokar kwadagon gyaran fuska.Ya shaida wa wata jarida cewa "Ba za mu janye kudirin dokar ba domin kuwa zai taimaka wajen gudanar da kasuwanci da samar wa 'yan kwadago karin dama."