Alan Pulido ya kubuta daga hannun wadanda suka sace shi

Mahukunta a Mexico sun yi bayani a kan yadda aka ceci kwararren dan kwallon kafar kasar, Alan Pulido daga hannun wadanda suka sace shi.

Jami'an gwamnatin suka ce Mr Pulido ya dambace daya daga cikin barayin da suka sace shi, kana ya dauki wayar salularsa ya kira 'yan sanda.

An bayyana cewa Dan kwallon kafar, wanda ke taka-leda wa kulab din Olympiakos na kasar Girka, ya ji rauni a hannunsa, lokacin da ya sa hannu ya banke kofar gidan da ake tsare da shi, ya yi kokarin tsira, kafin 'yan sanda su isa wurin.

A ranar Asabar din da ta gabata ne barayin suka yi wa motar Mr Pulido kawanya, bayan fitarsa daga wani wurin dabdala.