Nijar ta dukufa kan yakar ta'addanci

Image caption Jirage marasa matuka na kai hare-hare 40 a kowanne wata

Daga nesa a sararin samaniya a Niamey, babban birnin Nijar, wani kara ne ake iya jiyo wa.

A kasa kuma, dakarun soji ne ke atisaye, wani abu da suka yi ba adadi.

Yayin da karar inji da ake jiyowa a sararin samaniya ke karuwa, ashe wani abu ne mai kama da karamin jirgin sama.

Karar da ake ji ta wani jirgin sama mara matuki ne.

Sansani na 101, cibiya ce ta tattara bayanan sirri da rundunar sojin Faransa ta kafa a wani bangare na Operation Barkhane.

Muhimman ayyukan jiragen marasa matuka

Manufar jiragen marasa matuka da aka kaddamar da aiki da su a watan Fabrairu a shekarar 2014, ita ce su taimaka wa kasashe da ke yankin yaki da masu tsananin kishin Islama.

Jiragen kuma suna bada muhimmiyar gudunmuwa, wajen tattara bayanai daga sararin samaniya a kasashen yankin Sahel, ta hanyar amfani da shahararrun na'urorin daukan hoto, da na sadar da bayanai.

Kwararrun masu tattara bayanan sirri a sansanin na 101, sun dukufa wajen gano mayakan kungiyar IS da na Al-Qaeda dake yankin, AQIM.

Babban jami'in da ke kula da jirage biyar marasa matuka na Operation Barkhane, shi ne Laftanar Kanar Ben, kuma saboda dalilai na tsaro, ana amfani da suna daya ne wajen kiran sojojin Faransa.

Laftanar Kanar Ben ya bude kofar wani wuri mai kama da daki na karfe, kuma a ciki, akwai wuraren zama biyu, da na'urorin nuna bayanai daga sama, da madannai, da 'yan danjoji da sauran su.

"Daga nan wurin muke sarrafa kananan jiragen marasa matuka", Laftanar Kanar Ben ya ce.

Kaurar tarin jama'a

Kimanin hare-hare 40 ne ake kai wa da jirgin mara matuki a kowanne wata, inda a kan samu fiye da daya a kowace rana. A wannan wuri ne kwararru da Laftanar Kanar Ben ke jagoranta ke aikin sa'o'i shida-shida, kuma idanunsu kafe ga na'urorin dake nuna bayanai.

Yanzu, Nijar ta zama wata muhimmiyar kawa ga kasashen yammaci wajen yaki da ta'addanci. In aka dubi taswirar kasashen dake zagaye da kasar, za a ga dalilin haka.

Image caption Nijar ta zama wata muhimmiyar kawa ga kasashen yammaci wajen yaki da ta'addanci

Kasar ta na kewaye da makwaftan kasashe da zasu iya shafa mata matsalar tashe-tashen hankali.

Daga arewaci, kasar ta na makwaftaka ne da Libya wadda a 'yan watannin baya bayan nan ta zama wuri na tashin hankali. A yammaci kuma, Mali ce ke makwaftaka da kasar wacce ita ma ke fama da matsalar masu tsatssaurar akida. A gabashi kuma, kasar Chadi ce, wacce ke fadi tashi da tashe tashen hankali na cikin gida, sannan a kudanci kuma, uwa-uba Najeriya, wacce ke fama da matsalar Boko Haram.

Tashe tashen hankali a Najeriyar ya haifar da kaurar mutane da yawa, inda fiye da mutane dubu 200 suka gudu zuwa Diffa dake kudu maso gabashin Nijar.

'Yan kasuwa sun ji ba dadi

Diffa gari ne da al'amura suka ja baya sosai dake 'yan kilomitoci daga iyakar kasar da Najeriya.

Image caption Jama'a sun yi wa 'yan tsirarun albarkatun Diffa yawa

Dama can mutanen wurin suna fama da talauci, yanzu kuma jama'a sun yi wa 'yan albarkatun da ke wurin yawa.

A babbar kasuwar garin, akwai wani malami dake koyar da Turanci, Ousmane Oumara wanda ya ce, 'yan kasuwa sun ji ba dadi da abubuwan da ke faruwa a tsallaken iyaka.

"Abubuwa ba yadda suka saba kasance wa ba", ya ce. A kusa kuma, wani dan kasuwar hatsi ne wanda ya ce farashin masara da gero yana ci gaba da tashi saboda an dai na kawo su daga Najeriya.

"Wani lokaci ina jin karar harbin bindiga a wajen gari, kuma ina jin tsoro", inji Ousmane.

Ganin yadda ake samun karuwar mutane daga Najeriya, babu isasshen wuri da zasu zauna a Diffa. Saboda haka, dubban 'yan gudun hijira suna kokarta wa ne su samu wuri na wucin gadi.

Image caption Nijar na daya daga cikin kasashen duniya mafiya talauci

A wani sansanin 'yan gudun hijira dake gefen hanya, an kafa manyan tanti-tanti farare. Daga cikin su kuma, dariya kake ji tana tashi, da kururuwa ta yara.

Yaran, sun daga hannayensu sama, suna shewa, suna cewa: "Malam! Malam! Malam! Ina da amsar!"

Malamin kuma shi ne Mustafa Diri. Lokacin da aka tilasta mu shi barin kauyenshi, kilomita 8 daga iyakar Najeriya, bai so ya bar makarantar shi ba.

A saboda haka, sai ya tafi tare da makarantar ta sa.