Bauchi: Za a ba ma'aikata albashi

Image caption Dubban ma'aikata a Najeriya ba sa samun albashinsu a kan lokaci.

A Najeriya, gwamnatocin jihohi da dama na ci gaba da kiki-kaka da ma'aikatansu sabo da sun kasa biyan ma'aikatan albashi, wasu ma na watanni da dama.

Jihar Bauchi dai na daga cikin jihohin da matsalar ke haddasa tayar da jijiyoyin wuya matuka, inda ma'aikatan ke kukan cewa sun shiga mawuyacin hali, har ma suka yi wata zanga-zanga zuwa gidan gwamnati a 'yan kawanakin baya.

To sai dai Gwamnan jihar Bauchi, Barister Muhammad Abdullahi Abubakar, ya shaida wa wakilinmu Is'haq Khalid, cewa yana fatan za a kammala biyan ma'aikatan tarin albashinsu a cikin wannan mako, amma ya fara ne da karin bayani dangane da abin da ke kawo tarnaki ga biyan albashin ga kuma abinda ya ke cewa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti