Ana karancin abinci a Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana fama da yunwa a Nijar

Hukumar ayyukan agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya, UN OCHA, ta ce 'yan Nijar sama da miliyan biyu ne ke fuskantar matsalar karancin abinci a kasar.

Hukumar ta tabbatar da hakan ne cikin wani rahoto da ta buga game da sha'anin agaji a kasar ta Nijar.

Hukumomin kasar dai sun tabbatar da haka, kuma sun ce tuni suka yi tsarin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.

Daga Yamai wakilinmu Baro Arzika, ya aiko da wannan rahoton:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Karin bayani