Amurka ta yi gargadi game da gasar Turai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a fara wasan gasar cin kofin Turai a watan Yuni

Amurka ta gargadi 'yan kasarta game da yiwuwar kai hare-haren ta'addanci a nahiyar Turai yayin wasan kwallon kafa da za a yi a watan Yuni a Faransa.

A cewar ma'aiakatar tsaron Amurka, akwai yiwuwar kai hari a kan wuraren yawon bude ido da kantunan cin abinci da cibiyoyin kasuwanci da na sufuri.

Kazalika, ta kuma ce filayen wasa da wajen da za a yada shirin duk suna cikin hadari.

Gargadin ya kuma hada har da gasar tseren kekuna ta Faransa da za a yi a watan Yuli, da kuma bikin Ranar Matasa ta Darikar Katolika ta Duniya da za a yi a Poland.