An yi min wariyar launin fata — Benzema

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Benzema ya ce wariyar launin fata ce ta hana shigar dashi wasan kofin nahiyar turai

Daya daga cikin manyan 'yan wasan kwallon kafar Faransa, Karim Benzema, ya zargi mai horar da ayarin kwallon kafar kasar cewa wariyar launin fata ce ta hana shigar da Karim Benzeman a cikin ayarin da zai buga wa kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai da ke tafe.

Karim Benzema dai ya yi zarra ga baki dayan 'yan wasan kasar, kasancewar a halin da ake ciki ya fi kowa ci wa Faransa kwallaye, amma duk da haka bai samu shiga ayarin ba, bisa zargin cewa ya yi wa wani abokin wasansa sharrin da ya shafi lalata, amma kuma Karim Benzeman ya musanta.

A bara ne aka dakatar da shi daga ayarin.

Sai dai dan wasan ya shaida wa wata mujallar Spaniya, inda yake taka-leda wa kulab din Real Madrid cewa ana ci gaba da dakatar da shi daga ayarin ne, ba don wani abu ba, illa karuwar tasirin jam'iyyun siyasa masu kyamar launin fata a Faransa.