Koriya ta arewa ta bude dandalin Facebook na gwaji

Dandalin facebook na gwaji
Bayanan hoto,

Dandalin facebook na gwaji

An bude wani dandalin sada zumunta na gwaji a kasar Koriya ta arewa.

Dandalin dai ya dan bayyana ne a intanet ta adireshin StarCon.net.kp na wani gajeren lokaci, kana ya bace.

Babu cikakken bayani a kan wanda ya kirkiri adireshin StarCon.net.kp, amma ana kyautata zaton cewa wani shirin gwaji ne da ake sa ran kamfanin gidan wayar kasar ke yi da nufin bude dandalin a nan gaba.

Sai dai dandalin ya fuskanci matsala, kasancewar ana bude shi ba a je ko'ina ba masu kutse suka far masa, kuma daga nan shiga dandalin ya yi wuya.

Wani mai bincike a bangaren shafukar yanar-gizo na kamfanin Dyn mai suna Doug Madory ne ya gano dandalin, yana cewa ba kasafai ake bude shafukan sada zumunta a kasar Koriya ta arewar ba.

Mr Madory ya shaida wa BBC cewa a ganin sa ba a bude dandalin da nufin ba wa al'umar kasashen wajen damar shiga ba.