Wainaina ya sha duka a Jamus

Image caption Fitaccen marubuci dan kasar Kenya Binyavanga Wainaina

Fitaccen marubucin nan dan kasar Kenya, Binyavanga Wainaina ya ce wani direban tasi ya ci zarafinsa a birnin Berlin na kasar Jamus.

Wainaina ya ce lamarin ya bar shi cikin tunanin cewa don shi "bakar fata ne mai datti" shi ya sa direban ya ci zarafinsa.

"Na yi mamaki a ce abu kamar wannan zai faru da mutum iri na", marubucin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wainaina ya ce ya je Berlin ne a matsayin daya daga cikin marubuta da suka samu tallafin gidauniyar DAAD, kuma bayan ya kammala abin da ya kai shi ne, ya kira mai tasi daga gida domin ya kai shi inda ya ke son zuwa.

"Da yake bana iya magana da Jamusanci, kuma saboda ciwon bugun jini dana yi fama da shi a baya, maganata bata fita da kyau sosai. A haka dai na samu na kira kamfanin tasi, kuma suka turo mun direba", marubucin ya kara da cewa.

Wainaina ya ce "Da ganin direban tasin na san ba mai hakuri ba ne. Bayan mun fara tafiya, ya yi ta tambaya ta adireshin inda zai kai ni, ni kuma ina ta kokarin dubawa a waya ta in fada mushi".

Ya ce rashin fadawa direban adireshin a kan lokaci ya sa ya fusata, duk da cewa kudi za a biya shi na iya lokacin da aka bata mushi.

Marubucin ya ce daga nan ne direban ya tsayar da motar, ya je ta gefen shi, ya fara lakada mushi duka, tare da yin jifa da jakarsa.

"Babban abin takaicin kuma shi ne mutanen dake wuce wa ba su ce mun ko uffan ba", Wainaina ya kara da cewa.

Mutane da dama sun yi tsokaci ta shafin Twitter na Binyavanga Wainaina, inda Dina Ligaga ‎@dinoleegz ta ce "wannan abu ya yi muni sosai! In muna kasarmu, ba ma ganin yadda duniya ke hana nuna banbanci.