BH: An kashe mutane tara a Niger

Wasu mutane da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a garin Yebi a yankin Bosso na jihar Diffa a jumhuriyar Nijar, inda suka kashe mutane tara.

Kazalika wasu mutanen sama da 10 kuma sun jikkata.

Hukumomin jihar ta Diffa dai wadanda suka tabbatar da lamarin sun ce, wannan shi ne hari na biyu da aka kai a garin na Yebi kasa da makwanni biyu, duk da kusancinsa da Bosso, inda ke da sansanin sojoji.

Daga yamai wakilinmu Baro Arzika ya aiko da karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti