Sojojin Nigeria sun kama 'barayin mai'

Wani butun mai a yankin Niger Delta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fashe-fashen bututu da satar mai na barazana ga tattalin arzikin Nigeria

Jami'an tsaron Nigeria sun ce sun cafke mutane takwas da ake zargi da satar danyan man fetur da fasa bututu a yankin Naija-Delta.

An kama mutane uku da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a teku a wani sumame da jami'ai suka kai, a cewar kakakin rundunar sojin ruwa ta Nigeria Cor Ezekobe.

Ya kara da cewa rundunar ta kuma kama wasu mutane biyar 'yan kasar Benin a cikin wani kwale-kwale dauke da jarkokin man fetur.

Satar man fetur da fasa bututu ta karu a baya-bayan nan, abinda ya janyo raguwar kudaden shigar kasar da kuma karancin wutar lantarki.

Mr Ezekobe ya ce an kama 'yan kasar "Benin din ne da jarkoki 900 makare da man fetur na sata," inda ya kara da cewa za a gabatar da su a gaban kuliya bayan an kammala bincike.

Jami'an tsaron sun kuma ce sun lalata wata babbar matatar man fetur wacce ake amfani da ita wajen sarrafa danyan mai ba bisa ka'ida ba a Karamar Hukumar Burutu ta jihar Delta.

A baya dai ana alakanta irin wadannan laifuka ne ga masu tayar da kayar baya a yankin na Naija-Delta, sai dai kasancewar 'yan kasashen waje a sahun wadanda ake zargi da hannu a lamarin, na nuni da yadda lamarin ke kara kazanta.