Avengers sun sake fasa rijiyoyin mai

Masu fafutukar Naija Delta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fashe-fashen bututu da satar mai na barazana ga tattalin arzikin Nigeria

Masu tayar da kayar baya na kungiyar Niger Delta Avengers (NDA), sun ce sun fasa rijiyoyin mai guda biyu mallakar kamfanin mai na Chevron a Nigeria.

Wannan shi ne hari na baya-bayan nan da sabuwar kungiyar ta dauki nauyin kai wa.

Duk da cewa kamfanin Chevron bai tabbatar da harin ba, wani masani ya tabbatar da harin ga kamfanin dillancin labarai na AFP, yana mai cewa lamarin ya haifar da malalar mai.

Satar man fetur da fasa bututu ta karu a baya-bayan nan, abinda ya janyo raguwar kudaden shigar kasar da kuma karancin wutar lantarki.

NDA ta tabbatar da harin ne a shafinta na Twitter:

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption NDA ta zafafa kai hare a yankin Naija Delta

A wuri guda kuma, jami'an tsaron Nigeria sun ce sun kama mutane takwas da ake zargi da satar danyen man fetur da fasa bututu a yankin Naija-Delta.

An kama mutane uku da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a teku a wani samame da jami'ai suka kai, a cewar kakakin rundunar sojin ruwa ta Nigeria Cor Ezekobe.

Ya kara da cewa rundunar ta kuma kama wasu mutane biyar 'yan kasar Benin a cikin wani kwale-kwale dauke da jarkokin man fetur.

Mista Ezekobe ya ce an kama 'yan kasar "Benin din ne da jarkoki 900 makare da man fetur na sata," inda ya kara da cewa za a gabatar da su a gaban kuliya bayan an kammala bincike.

Jami'an tsaron sun kuma ce sun lalata wata babbar matatar man fetur wacce ake amfani da ita wajen sarrafa danyan mai ba bisa ka'ida ba a Karamar Hukumar Burutu ta jihar Delta.