Manahajar taimaka wa masu cutar mantuwa

Hakkin mallakar hoto Duke University

An kaddamar da wata manahaja da za ta taimaka wa masu cututtkuan kwakwalwa daban-daban kamar irin su cutar mantuwa.

Wata kungiya mai taimakawa masu fama da cutar mantuwa da ke Birtaniya ce ta kirkiro wanann hanya.

Kwararru irin su Tula Brannelly ta jami'ar Southampton na lale marhabun da wannan ci gaba.

Ta ce '' Mutanen da ke fama da cutar mantuwa za su cigaba da neman taimako daga gare mu, kuma sanin me zai iya faruwa da su zai kara mana karfin guiwar yadda za mu taimaka.

Wata mata da ke fama da wannan cuta ta mantuwa ita da mijinta sun shaidawa BBC dalilan da suka sa suke goyon bayan wannan kirkira da aka yi.