Amnesty na son Ecowas ta dakatar da Gambia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin shugaba Yahaya Jameh da cin zarafin dan adam

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty, ta yi kira ga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, da ta dakatar da Gambiya, muddin ba'a samu cigaba a yanayin kare hakkin bil adama ba a kasar.

Kungiyar Amnesty ta ce gwamnatin Gambiya ta nuna rashin imani a kokarin murkushe 'yan adawa yayin zabukan da aka yi a watan Disamba.

An ce daya daga cikin 'yan dawar ya rasu a hannun jami'an tsaro bayan gana masa azaba da aka yi.

A makon da ya gabata ne shugaba Yahya Jammeh ya ce ba zai bayar da umarnin yin bincike ba.

Ya ce ba sabon abu bane mutuwar fursunoni lokacin da suke tsare.