Barkindo ya zama Sakatare Janar na OPEC

Muhammed Barkindo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barkindo ya taba zama mataimakin Sakatare Janar na OPEC a 2006

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC, ta sanar da Mohammed Barkindo daga Najeriya a matsayin sabon Sakatare Janar na kungiyar.

Barkindo, wanda aka zaba a ranar Alhamis, zai maye gurbin Abdalla El-Badri dan kasar Libya ne, wanda ke rike da mukamin tun shekarar 2007.

Wannan al'amari dai ya zo ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.

Haka kuma akwai rikicin siyasa tsakanin kasashen Saudiya da Iran, wadanda dukkansu suna da arzikin mai, na neman ikon fada a ji a Gabas ta Tsakiya.

Mr Barkindo ya taba zama shugaban kamfanin samar da mai na Najeriya, NNPC, daga shekarar 2009 zuwa 2010.

Ya kuma taba zama mukaddashin Sakatare Janar na kungiyar ta OPEC a 2006.