IS: An kama mutum shida a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP

Mahukunta a Burkina Faso sun cafke wasu mutum shida da ake zargin suna da hannu a wani harin da mayakan IS suka kai birnin Ouagadougou a watan Janairun da ya wuce.

Sama da mutum 30 suka mutu, yayin da mutum 70 suka jikkata, lokacin da 'yan bindiga suka bude wuta a kan jama'a a wani Otel da wata mattatarrar jama'a da ke tsakiyar birnin.

Cikin wata sanarwa, rundunar 'yan sandan kasar ta ce mutanen da aka kama 'yan kasashen waje ne, wadanda suka ba wa maharan masauki, tare da taimaka musu wajen yin aika-aikarsu.