An samu wasu da laifin kashe Musulmi a India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kotun ta kuma wanke mutum 36 daga laifi

Wata kotu a jihar Gujarat da ke India ta samu mutum 24 da laifin karkashe Musulmi da dama.

Ana yi wa kisan kallon ta'asa mafi girma da aka yi a ƙasar tun bayan samun 'yancin kan ƙasar.

Wata kotu ta musamman ta samu mutum 11 daga cikinsu da lafin kisan kai.

Kotun ta kuma wanke mutum 36 daga laifi.

A shekarar 2002 ne kotun kolin kasar ta bayar da umarni a sake yin bincike kan kisan Musulmi 69, wadanda ke zaune a wani gida a birnin Ahmedabad.

An maƙure mutanen ne har sai da suka mutu, kana aka ƙona gawarwakinsu.

Lamarin ya auku ne lokacin da Fira Minista Narendra Modi ke jagorancin Gujarat a matsayin gwamna, ko da ya ke ya sha musanta zargin cewa bai ɗauki mataki kan lamarin ba.

  • Mutum 69 ne suka mutu a harin na 28 ga Fabreru 2002
  • An kuma yashe da kona gidaje da shaguna
  • Mutane 66 ka tuhuma da laifi - shida sun mutu kafin shari'ar
  • An fara shari'ar ne a watan Satumbar 2009
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hargitsin na 2002 na daya daga cikin mafi muni a India
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Modi ya dada yana musanta hannu a lamarin