Aikin ɗan sanda: An tantance mutane 338,227

Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta Nigeria ta sanar da cewa, ta tantance mutane 338,227 waɗanda daga cikinsu ne za a zaɓi mutane 10,000 da za a ɗauka aikin ɗan sanda.

Mutane 911,438 ne suka nemi cika takardun neman aiki, amma aka zubar da mutane 573,211 yayin tantancewa matakin farko.

Shugaban hukumar kula da ayyukan 'yan sandan, Mike Okiro ne ya sanar da hakan a Abuja, inda kuma ya ce, yanzu za a je ga mataki ne gaba.

Waɗanda aka tantance yanzu zasu mataki na gaba inda za a yi wata tantancewar a matakin jiha daga ranar 6 ga wata Yuni.

'Yan sandan da za a ɗauka dai sun haɗa da ƙananan 'yan sanda, da kuma jami'ai.

Bayanai sun nuna cewa, jihar Benue ce take da masu neman aikin mafiya yawa, wato 29,000 inda jihar Kogi take biye mata da masu neman shiga aikin ɗan sanda 19,000.

Jihar Lagos ce ta ke da masu neman aikin mafiya ƙaranci wato mutane 2000.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin a ɗauki ƙarin 'yan sanda 10,000 domin ƙarfafa tsaro, da kuma samar da aikin yi ga matasa.

Cewar mutane kusan miliyan guda sun nemi guraben aiki 10,000 ya ƙara fito da ƙamarin matsalar rashin aikin yi a Nigeria.