Rasha: An kama masu satar bayanai

Hakkin mallakar hoto thinkstock

A Rasha, an kama mutum 50 da ake zargi da amfani da fasahar satar shiga rumbun bayanai na kwamputa inda suka sace dala miliyan 18.

Gungun mutanen da aka kama dai suna amfani ne da fasahar da ke bude bayanan sirri, wanda kuma ya basu damar samun bayanan asusun ajiyar banki.

Mutanen an kuma ce sun yi amfani da dabara mai tasirin gaske da dabarun tsaro na computer basa iya karyawa.

Kamfanin harkar tsaro na Rasha IB ya ce waÉ—anda aka kama gungun wadanda aka kama din sun jima suna satar bayanai ta intanet.