Taƙaddama kan ɗaura ɗankwali a Afrika Ta Kudu

Wata taƙaddama ta ɓarke a kafofin sada zumunta na intanet a Afrika Ta Kudu, bayan da wata ma'aikaciyar gidan talbijin na tashar eNCA ta ce an ƙi nuna ta a wani rahotonta saboda tana sanye da ɗankwali, wanda ake kira da suna doek.

Tashar talbijin ɗin dai ba ta fadi ko wannan ne dalilin da ya sa aka ƙi saka rahoton ba, amma a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa wakiliyar tasu Nontobeko Sibisi, ta sanya ɗankwalin ne ba tare da neman izinin shugabanninta ba.

Ko ma dai menene dalilin, to al'amarin ya jawo zazzafar muhawara a kan sanya tufafi da wariyar launin fata.

Sanya ɗankwali ko mayafi al'ada ce ta yawancin mutanen Afrika, amma a yanzu ta zamo abin ado wajen waɗansu.

Ma'aikatan tashar eNCA sun yi ta wallafa hotunansu sanye da ɗankwali a shafin Twitter, domin nuna goyon baya ga abokiyar aikin nasu.

Wasu ma da ba ma'aikatan gidan talbijin ɗin ba sun bi sahu:

Wata mai amfani da shafin Twitter ma ta sanya hoton Nelson Mandela ne sanye da ɗankwalin doek domin nuna dalilinsu da ya sa suke girmama mayafi.