An bukaci MDD ta kai abinci Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

Amurka da Faransa da kuma Birtaniya sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da jirgin sama wajen jifa kayan abinci a yankunan da aka yi wa kawanya a Syria.

Sun ce gwamnatin shugaba Assad ta ki martaba ranar jiya, wato daya ga watan Yuni a matsayin ranar da za a rarraba kayan agaji a kasar.

A ranar Laraba ne wani ayarin motoci ya isa garin Daraya, wanda sojojin gwamnatin Syria suka yi masa zobe na tsawon shekara hudu, amma ayarin bai kai kayan abinci ba, ko da loma guda.

A gobe ne ake ran Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama don tattaunawa a kan maganar jefa kayan agaji ga al'umomin da aka musu kawanya.