Haren-haren ta'addanci 'ya ragu' a duniya

Image caption Kungiyar IS ta kai hare-hare da dama kasashe daban-daban

Wani rahoto da gwamnatin Amurka ta fitar ya ce hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a yankin tafkin Chadi ya ragu sosai.

Rahoton ya ce hakan ya faru ne sakamakon matsin lambar da 'yan kungiyar ke fuskanta daga sojojin Nigeria da dakarun hadin gwiwa na kasashen yankin tafkin Chadi.

Kazalika, ya kara da cewa hare-haren ta'addanci da kungiyar IS da sauran kungiyoyi ke kai wa a kasashen duniya ma ya ragu da kashi 14 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Rahoton ya ce sai dai kungiyar IS ita ce har yanzu take kai munanan hare-hare take kuma kara samun gindin zama a kasashen Libya da Masar.

Alkaluman da ma'aikatar tsaro ta Amurka ta fitar, sun nuna cewa an samu hare-haren ta'addanci 981 a duk wata a fadin duniya a shekarar 2015, inda aka kashe mutane 28,328 a cikin shekarar.