'Tsoffin manyan jami'an FIFA sun azurta kansu'

Hakkin mallakar hoto AP

Lauyoyin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA sun ce tsoffin manyan jami'an hukumar, Sepp Blatter, da Jerome Valcke da Markus Kattner sun aikata almundahana.

Sun ce tsoffin jami'an sun yiwa kansu aringizon biyan kansu dala miliyan 80 ko kuma fan miliyan 55 a cikin shekaru biyar.

Kwana guda bayan samamen da 'yansandan Switzerland suka gudanar, hukumar ta FIFA ta bayyana kwantaragin na tsohon shugaban hukumar Mr Blatter, da sakatare janar da hukumar da aka kora Mr Valcke, da kuma tsohon daraktan kudi Mr Kattner da aka sallama.

Lauyoyin FIFA sun ce akwai shaidun da suka nuna cewa su duka ukun sun hada kai tare da azurta kan su a tsakanin shekara ta 2011 da 2015.

A cikin watan Fabrairu ne kwamitin ladabtarwa na hukumar ta FIFA ya dakatar da wadanda ake zargin Blatter da Valcke har na tsawon shekaru 6 da 12 ko wannensu.

Dukakkninsu dai sun musanta aikata ba daidai ba.

Tun a cikin watan Mayun shekara ta 2015 ne hukumar ta Fifa ta fada cikin rudani, lokacin da binciken da Amurka ta gudanar ya bankado gagarumar badakalar cin hanci a tsakanin manyan jami'an hukumar.