An kashe matar da ta yi 'ɓatanci' ga Annabi a Kano

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Rundunar 'yan sanda ta ce za ta hukunta duk wanda aka samu da hannu kan lamarin.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta kama mutum daya, bayan kashe wata mata da aka zarga da yin ɓatanci ga Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW).

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kano, Magaji Musa Majiya, ya shaida wa BBC cewa mutanen sun kashe matar ne, kana suka yi yunkurin kashe mijinta a kasuwar Kofar Wambai da ke birnin na Kano.

Ya kara da cewa mutum na biyu da ake zargi da kashe matar ya mika kansa ga 'yan sanda dazu, Inda ya bayyana musu abin da ya faru.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce a yanzu haka sun fadada bincike kan batun.

A cewarsa, jami'an tsaro sun ceci mijin, kuma yanzu haka yana hannunsu.

Rahotanni dai sun ce harkoki sun ci gaba da tafiya kamar yadda ya kamata bayan faruwar lamarin.

Sai dai an jibge jami'an tsaro a wurare da dama na birnin na Kano, musamman masallatan juma'a.