Muhammad Ali ya rasu

Hakkin mallakar hoto Reuters

Fitaccen zakaran damben duniya da ya kafa tarihi, Muhammad Ali ya rasu.

Kafin nan dai ya kwanta a asibiti a jihar Arizona dake Amurka. Ya rasu yana da shekaru 74.

Dattijon yana fama ne da cutar da ta shafi numfashi, wadda kuma cutar tsufa ta kyarma ke ƙara ta'azzara ta.

Yayi ritaya daga dambe ne a shekarar 1980, amma a baya bayan nan yana fama da rashin lafiya, inda koda a farkon bara sai da ya kwanta a asibiti.

Sunansa na ainihi dai shi ne Cassius Clay, amma ya koma Muhammad Ali bayan ya zama musulmi a shekarar 1964 lokacin da karon farko ya zama zakaran damben duniya.

An dai janye lambar bajinta da yake da ita bayan ya ƙi yin zuwa Vietnam, amma ya sake ceto matsayin bayan shekaru goma lokacin da doke George Foreman a damben da ake yi wa taken 'karon battar ƙarfe.'

An haifi Muhammad Ali ne a shekarar 1942.