Boko Haram ta kashe sojojin Nigeria da Niger

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeriya da Nijer sun sha fadin cewa suna samun nasara a kan 'yan Boko Haram

An kashe sojojin Niger 30 da kuma na Nigeria biyu a wata fafatawa da suka yi da mayakan Boko Haram a garin Bosso na Nijar.

Ma'aikatar tsaro ta Niger ta ce daruruwan mayakan Boko Haram ne suka kai hari kan wani sansanin sojoji da ke garin, wanda ke kan iyakar kasar da Nigeria, a daren Juma'a.

Sai dai ta ce sojojin sun mayar da martani a ranar Asabar da safe inda suka sake kwace iko da sansanin na su.

An kuma kashe maharan da dama tare da raunata wasunsu.

Garin na Bosso ya sha fama da hare-haren Boko Haram a baya, abinda ya sa hukumomi suka kafa dokar tabaci a yankunan da ke Kudancin kasar.

Dakarun Niger na cikin rundunar hadin gwiwa da ke fafatawa da mayakan Boko Haram a yankin tafkin Chadi.