DRC: Me yiwuwa a yi zaben raba gardama

Hakkin mallakar hoto

Wani babban jami'in jam'iyyar PPRD mai mulki a jamhuriyar dimukradiyyar Congo yayi kalaman dake cewa, mai yiwuwa ayi zaben raba gardama a kasar.

Hakan kuma ka iya baiwa shugaba Joseph Kabila damar tsaiwata mulkinsa.

Henri Mova Sakani, wanda shi ne sakatare janar na jam'iyyar ya bayyana hakan ne yayin wani gangami a Kinsasha domin bikin zagayowar ranar haihuwar shugaba Kabila.

Matakin tsawaita mulkin shugaba Joseph Kabila dai zai iya kawo sa…ďani da 'yan adawa da kuma kasashen yamma da suka dage cewa, shugaba Kabila ya sauka daga mulki bayan ya kammala wa'adinsa na biyu.

Joseph Kabila dai yana mulkin kasar tun daga shekara ta 2001 bayan kisan mahaifinsa.