An kashe 'yan jarida a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Gilkey da abokan aikinsa sun mutu sakamakon harin roka.

Wani dan jarida ba Amurke da tafintansa dan Afghanistan sun hallaka yayin da suke tafiya tare da dakarun kasar a kudancin lardin Helmand.

Mahukuntan Afghanistan sun ce David Gilkey - wanda ke aiki da gidan rediyon al'umma da ke Amurka da tafintar nasa Zabihullah Tamana sun mutu ne bayan da harin roka ya samu motarsu lokacin da mayakan Taliban suka yi musu kwanton-bauna.

Harin ya kuma hallaka direban motar wanda sojan Afghanistan ne.

Wata sanarwa da mahukuntan tsaron suka fitar ta ce yan jaridar biyu na kan hanyarsu ta zuwa wani aiki ne tare da sauran ma'aikata biyu da ba su samu ko da kwarzane ba.