Ellen Sirleaf ce sabuwar shugabar Ecowas

Image caption Kasashen yammacin Afrika na fama da hare-hare

An zabi shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf, a matsayin sabuwar shugabar kungiyar Ecowas.

An yi wannan zabe ne a wani taro da shugabannin kasashen yammacin Afrika ke yi a Dakar babban birnin Senegal.

A wajen taron dai shugabannin kasashen Afrika ta yamman sun tattauna kan samar da dakaru na musamman domin kawo karshen hare-haren masu da'awar jihadi a yankin.

Masu tayar da kayar baya da ke da alaka da Al Qaeda sun kaddamar da hare-hare a Mali da Ivory Coast da Burkina Faso, yayin da kungiyar Boko Haram kuma take kai nata hare-haren Najeriya da makwabtanta.

Sai dai shugabannin yankin Afrika ta yamman basu yi wani karin bayani kan rundunar ba.

Sun kuma yi kira da a tabbatar da an yi sahihin zabe a Gambiya, sun kuma ce ya kamata dakarun tsaro su guji amfani da karfi kan fararen hula yayin zaben.