An rataye mai yi wa mata fyade a Iran

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An sha rataye masu aikata mugayen laifi a Iran

Hukumomin kasar Iran sun rataye wani mutum da aka kama da laifin yi wa gomman mata fyade a kudancin birnin Shiraz.

Sunan mutumin Amin ''D''.

Amma an fi saninsa da "Vaseline Man" saboda dabi'arsa ta shafe jikinsa da basilin a duk lokacin da zai haura gidan mutane da daddare don yin fyade.

An sha kokarin kama shi, amma sai a karshe aka samu nasarar yin hakan da taimakon kamarar CCTV da kuma shaidar gwajin kwayoyin halitta.