Ce-ce-ku-ce kan mutuwar Ali a Amurka

Marigayi Muhammad Ali
Image caption Ya rasu ne sanadiyyar cutar da ta shafi numfashi.

Rasuwar Muhammad Ali ta janyo cece-kuce a siyasar Amurka, tsakanin masu neman takarar shugabancin kasar.

A sakon ta'aziyya da ya aike, dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump, ya bayyana Ali a matsayin wani jan gwarzo da za a dade ba a manta da shi ba da samun wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai a nasa bangaren dan takara karkashin jam'iyyar Democrat Sanata Bernie Sanders, ya zargi Mista Trump da yin munafunci.

A shekarar da ta gabata ne marigayi Ali, ya yi Allah-wadai da kalaman da Mista Trump ya yi na a haramtawa Musulmai shiga Amurka.

Ita ma Hillary Clinton ta ce Mista Trump bashi da alkibla a kalamansa.

A bangare guda kuma iyalan Muhammad Ali sun sanar da cewa ranar juma'a ne za a yi jana'izar mamacin.