An kai harin sama kan 'yan tawaye a Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters

A kasar Syria rahotanni na cewa ana kai hare-hare ta sama kan yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawaye a kusa da birnin Aleppo.

An dai ambato ma'aikatan kungiyoyin agaji na cewa a kalla an fito da gawarwaki 20 daga wurare daban-daban inda aka kai harin.

Akwai kuma wasu rahotanni daga bangaren jami'an gwamnati masu rike da wani bangare na birnin da ke cewa 'yan tawaye sun harba wata roka a birnin.

Kafar watsa labarai ta gwamnatin kasar na cewa an kashe a kalla mutane 24 a harin na ranar Asabar.