Niger: Boko Haram ta sake kwace Bosso

Barnar Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram na yawan kai hare-hare Nijar a baya-bayan nan

Kungiyar Boko Haram ta sake kwace iko da garin Bosso da ke Kudu maso Arewacin jamhuriyyar Nijar.

Magajin garin Bosso da wata majiya ta soji ce ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Majiyar ta kara da cewa hakan ya faru ne bayan fafatawar da mayakan kungiyar suka yi da dakarun Najeriya da Nijar din.

Da farko dai mayakan sun kwace iko da garin ne da ke kusa da iyakar Najeriya a ranar Juma'a, inda suka kash sojojin Najeriya da Nijar 30.

A ranar Asabar kuma sojoji suka kwato ikon garin, amma ba a dauki lokaci ba mayakan na Boko Haram suka sake kwace shi.

A baya-bayan nan dai hare-haren kungiyar Boko Haram na kara yawa a jamhuriyyar Nijar, bayan da hare-haren da suke kai wa Najeriya suka ragu, sakamakon luguden wutar da sojojin kasar suke kai musu.