Wani kamfanin China ya sayi Inter Milan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Inter da AC Milan suna amfani da filin San Siro domin murza-leda

Wani kamfanin China ya amince zai sayi kaso kusan 70 cikin dari na hannun jarin Inter Milan ta Italiya.

Suning Commerce Group Co Ltd, zai biya fam miliyan 220 na manyan hannun jarin kungiyar, wanda tana daga cikin kunshin yarjejeniyar fam miliyan 590.

Erik Thohir zai ci gaba da zama shugaban kungiyar, amma za a rage masa hannun jarinsa zuwa kashi 31 cikin dari.

Kamfanin zai bayar da kudaden da za a kara hannun jari a Inter Milan, wanda hakan zai taimaka a sayo manyan 'yan wasan kwallon kafa.

Michael Bolingbroke zai ci gaba da zama a babban jami'in kungiyar, yayain da Roberto Mancini zai yi zamansa a matsayin kociyan Inter Milan.

Shi kuwa tsohon shugaban kungiyar Massimo Moratti zai bar kungiyar zai kuma sayar da hannun jarin da yake da su da suka kai kashi 30 cikin dari.