Masu satar bayanai sun shiga shafin Zuckerberg

Mark Zuckerberg Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Facebook Mark Zuckerberg

Duk da cewa shi ne shugaban shafin sada zumunta mafi girma a duniya amma duk da haka sai da masu satar bayanai suka shiga cikin shafukan Mark Zuckerberg.

Masu satar bayanai sun shiga cikin shafin Zuckerberg na Intagram da Twitter da,Linkedin da kuma Pinterest a ranar Lahadi.

Wani gungu na masu satar bayanai da ke da magoya baya sama da 40,000 a shafin Twitter ya dauki alhakin kai harin.

Masu satar bayannan sun dinga cika baki kan harin da suka kai a shafin Tweeter inda suka gayyaci Zuckerberg kan ya kirasu.

Sai dai tuni aka cire abubuwan da aka turo a shafinsa na Twitter.

Tun a shekara ta 2012 Mr Zuckerberg ya dakatar da aikewa da sako a shafinsa na Twitter .