Euro 2016: Dan Faransa ya so kai hari

Hukumar lekan asiri ta Ukraine ta ce wani dan kasar Faransa da aka tsare a watan da ya gabata a lokacin da aka gano yana dauke da makamai ya so ya kai hari a lokacin Euro 2016.

Mutumin, wanda kafafen yada labarai na Faransar suka bayyana a matsayin Gregoire mai shekara 25, an kama shi ne a iyakar kasar Ukraine da Poland.

Shugaban hukumar leken asiri ta SBU, Vasyl Hrytsak, ya ce mutumin ya yi niyyar shirya hare-hare 15.

Ya kara da cewa Gregoire na dauke da bindigogi da dama da na'urorin da ke tayar da bama-bamai da kuma wasu abubuwan da ke tashin bama-baman.

Rahotanni sun ce a baya dai mutumin ma'aikacin kungiyar zuba adashin manoma a yankin Lorraine da ke gabashin Faransa ne.

Ba a taba kama shi da wani laifi ba a baya .