'Za a gyara kabarin Annabi Isa a Kudus'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mabiya addinin Kirista na zaton kabarin na Annabi Isa ne

Wata tawagar kwararru ta soma ayyukan gyara wani kabari da ke birnin Kudus, inda mabiya addinin Kirista suke zaton nan ne makwancin Annabi Isa Alaihis salam.

Wannan aiki na zuwa ne bayan fiye da shekara 200.

Za a soma gyaran ne a cikin cocin Holy Sepulchre, da tabbatar da tsayuwar ginin kushewar mafi daraja ga mabiya addinin Kirista.

An dan jinkirta ayyukan a dalilin jayyaya da ke tsakanin dariku ukun da ke kula da cocin.

Manyan limamai daga Greek Orthodox da Roman Katolika da Armeniyawa, sun ajiye bambance-bambancen da ke tsakanin su a waje guda, bayan fahimtar bukatar da ke akwai ta fara gyaran.