LRA ta sace mutane '100' a DR Congo

Sojojin LRA Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama ne suka salwanta a hannun kungiyar LRA

A kalla mutane 100 aka sace lokacin da wasu mayaka da ake zaton ‘yan kungiyar ‘yan tawaye ta Lord's Resistance Army (LRA) ne, suka kai sumame a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Kimanin ‘yan bindiga 50 ne suka kai harin a arewacin Kisangani, a karshen mako, kamar yadda gidan rediyon Okapi, mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ya rawaito.

Cikin wadanda aka sace har da dalibai ‘yan makaranta da ke rubuta rajabawar kammala makarantar firamare.

Hakazalika akwai ‘yan kasuwa da ma’aikatan lafiya wadanda ke gudanar da ayyukan allurar riga-kafin cutar kyanda.

Shugaban mulki na yankin Bondo, inda lamarin ya auku, ya ce jami’an tsaro na farautar maharan a dajin Adama, inda ake tsammanin shi ne maboyar ‘yan tawayen.

An kafa kungiyar LRA ne a Arewacin Uganda kusan shekaru 30 da suka wuce, sai dai ta koma Jamhuriyar Congo da wasu kasashe bayan da ta fuskanci matsin lamba daga jami’an soji.