An yi kutse ga kararrawar tsaron Mitsubishi

Mitsubishi ya sayar da motarsa samfurin outlander masu yawa

Asalin hoton, Mitsubishi

Bayanan hoto,

Mitsubishi ya sayar da motarsa samfurin outlander masu yawa

Masu bincike sun gano cewa ana iya kashe kararrawar tsaro na motar Mitsubishi samfurin Outlander ta hanyar intanet ta wi-fi da ke gaban motar.

Wannan raunin kenan ka iya ba wa barayi damar balla kofar motar su sace ta.

Haka kuma za a iya amfani da raunin wajen wargaza tsarin wasu na'urorin da ke jikin motar ta yanda batirin motar zai yi sanyi.

A halin da ake ciki dai kamfanin Mitsubishi ya bukaci masu motar da su dinga kashe na'urar intanet ta wi-fi da ke cikin motar har zuwa lokacin da zai kammala bincike.

Zuwa yanzu dai kamfanin Mitsubishi ya sayar da motarsa samfurin Outlander 100,000.