Boko Haram: Ana makoki a Nijar

Hakkin mallakar hoto boko haram
Image caption Mahukunta sun ce sojojin Nijar 22 mayakan Boko Haram suka kashe.

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar, sun ayyana zaman makoki na kwana uku domin nuna alhini ga sojoji da kuma al'umar kasar da suka halaka a wani hari da mayakan Boko-Haram suka kai garin Bosso, a Jihar Diffa da ke kudu maso gabshin kasar.

Kazalika gwamnati ta musanta cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun sake karbe iko da garin .

A taron da Majalisar ministocin kasar ta yi ta ce sojojin Nijar 22 da kuma na Nijeriya 2 aka kashe ya yinda mutane sama 100 suka jikkata a harin.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari garin, inda suka kashe sojojin kasar da dama, ciki har da sojojin Najeriya.